Yajin aikin likitoci: Ya kamata Buhari ya gaggauta tsige Ministan Lafiya – Gololo

Minista Ehanire

Daga FATUHU MUSTAPHA a Abuja

Jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Barrister Garus Gololo, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta tsige Ministan Lafiya, Dr. Osagie Ehanire.

Da yake zantawa da wakilinmu a Anbuja, Gololo ya ce ‘yan Nijeriya ba su taɓa sa ran ganin likitoci sun tafi yajin aiki ba a irin wannan lokaci. Yana mai cewa Shugaba Buhari ya bada isassun kuɗaɗe don yaƙi da annobar korona har da ƙarin tallafin da aka samu daga hannun ɗaiɗaikun mutane.

A cewar Gololo, “Me ya sa suka bari likitocinmu suka shiga yajin aiki? Gaskiya ya kamata a tsige minista; sannan a kama shi da laifin duk wani mara lafiya da ya rasa ransa.

“Tun tuni ‘yan Nijeriya sun gano rashin cancantarsa na zama minista. Duk da Shugaban Ƙasa ya bada kuɗaɗen da ake buƙata me ya sa ba za su iya biya wa likitocin buƙatunsu daga kuɗin ba?

“Idan kuwa ba a tsige ministan lafiyar da ire-irensa da ba su taɓuka komai ba, ni da kaina zan jagoranci tawagar lauyoyi mu yi zanga-zanga zuwa kotu don kuwa wannan abin kunya ne ga ƙasa.”

Ya ƙara da cewa, “Ya kamata a bai wa fannin shari’a da kuma ƙananan hukumomi cin gashin kansu domin ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

A ƙarshe, Gololo ya yaba wa Shugaba Buhari bisa naɗin da ya yi wa Usman Alƙali Baba a matsayin muƙaddashin Babban Sufeton ‘Yan Sanda (IGP), tare da cewa irin wannan mataki shi ne ya dace a ɗauka a kan ministan lafiya.