‘Yan ƙasa ga Tinubu: Ba ma buqatar tallafin rage raɗaɗi, a rage mana farashin fetur kawai

*A zuba kuɗin tallafin rage raɗaɗi zuwa harkar ilimi da lafiya – ‘yan ƙasa
*Tallafin rage raɗaɗi ba shi da wata ma’ana – Inji ɗan kasuwa
*Dole gwamnati ta sake tunani – Kwamared Alifia

Daga AMINA YUSUF ALI

A ƙoƙarinta na rage raɗaɗi da wahala da ‘yan ƙasa suke sha a sakamakon cire tallafi a kan man fetur, gwamnatin tarayya ta shigo da tsarin ba da tallafin rage raɗaɗi, amma ‘yan Nijeriya da suka samu kansu cikin matsuwa irin ta tattalin arziki sun fito sun bayyana cewa, sun fi qaunar a rage farashin man fetur fiye da tallafin rage raɗaɗin.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu a jawabinsa na amsar mulki ranar 29 ga watan Mayu ya bayyana cewa, a cikin kasasfin kuɗin shekarar gabaɗaya ba a ware kuɗin da za a cigaba da biyan tallafin mai ba.

Wannan furici nasa ya sa farashin man ya yi tashin gwauron zabi daga Naira 195 zuwa Naira 537 kowacce a lita kuma a lokaci guda ƙarin ya samu.

Wannan sabon farashin man ya yi sanadiyyar tsadar abubuwan rayuwa ga talakan Nijeriya kamar, kuɗin sufuri, tsadar kayan abinci da na masarufi, wannan ya tsunduma talakawa cikin ƙunci sosai.

A halin yanzu ma dai ko a gidajen mai mallakin kamfanin rarraba man fetur na Nijeriya NNPL ana sayar da shi a kan farashin Naira 614, Naira 615, da kuma Naira 617 a kan kowacce lita guda.

Domin rage wa talakawa wannan duka na ƙuncin rayuwa, Gwamnatin tarayya ta ƙirƙiro da dabarar tallafin rage raɗaɗi. Wato ta kasafta Naira biliyan 5 na rage raɗaɗi ga kowacce jiha a ƙasar har ma da birnin tarayyar Abuja.

Gwamnatin Tarayya ta ba da wannan kuɗaɗen ne don a gwamnonin jihohi su sayi Kayayyakin abinci don raba wa talakawansu.

Sai dai kuma wasu ‘yan Nijeriya yayin zantawarsu da jaridar Blueprint a ƙarshen makon da ya gabata sun bayyana cewa, su sam gara a rage farashin man fetur a kan duk wani tallafin rage raɗaɗi da za a bayar.

A cewar wasu ma tallafin zai iya shigewa aljihun masu ruwa da tsaki kaɗan ne ma wataƙila zai zo wajen talaka.

Wani mazaunin Abuja mai suna Ibrahim Bernard, ya bayyana wa Blueprint cewa, gara a rage farashin mai sau dubu a kan wannan tallafin rage raɗaɗin.

A cewar sa, shi kansa motocinsa biyu da yake hawa yanzu ya gagara hawansu saboda ba zai iya cigaba da sa musu mai ba.

A cewar sa, wahala ta yi yawa a Nijeriya, ba kowa ke iya cin abinci sau uku ba ma a rana, saboda matsin tattalin arziki.

A don haka yake shawartar gwamnatin tarayya a kan ta rage farashin mai.

Shi kuma matuƙin tasi, Jamilu Usman, ya roƙi shugaba Tinubu da ya yi amfani da tallafin man ya gyara harkar lafiya da ta ilimi a ƙasar.

Domin a cewar sa ɗan Nijeriya ba ya amfana da komai a Tallafin man. Su kansu fetur ɗin yana hana su tafiyar da sana’arsu ta tasi yadda ya kamata. Domin ba wata riba a yanzu.

Shi kuma ɗan kasuwa, Sulaiman Bala, a ra’ayinsa ya ce ba da tallafin raɗaɗi ba shi da wata ma’ana kuma ma a ganinsa ba shi da wani alfanu tunda mutane suna shan wahala a sanadinsa.

Kuma ya yi kira ga ‘gwamnati da ta ba wa ‘yan ƙasa jari shi ya fi. Sannan ta yi ƙarin albashi kuma ta samar da ayyukan yi.

Shi wannan tallafin rage raɗaɗi abu ne na rana ɗaya kuma ba abinda zai ƙara wa mutane.

Mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum na gwamnati, Shukuroh Tiamiyu, ya gaya wa majiyarmu cewa, wannan tallafin rage raɗaɗin ba zai tava zama maslaha ba ga matsalolin da suke addabar talakawa. Ya yi kira da a rage farashin mai domin shi ne maslaha.

Shi kuma Kwamared Sunday Alifia, ya nemi Tinubu da ko dai ya mayar da tallafin mai, ko kuma ya rage farashin mai raga-raga don amfanin talakawa.

A cewar sa, kuskure ne wanda an riga an tafka. Da Tinubu yake ganin zai iya ba da tallafin rage raɗaɗin da zai rage wa al’umma zafi. Domin wannan abu ba wani abu ya jawo ba sai saka al’umma a cikin tsaka mai wuya.

Domin a cewar sa, cire tallafin mai ba tare da an tsara masa ba shi ne abinda ya jefa ‘yan ƙasa cikin halin ha’ula’i. Don haka a cewar sa, ya kamata gwamnatin ta sake nazari a kan wannan tsari nata.

A cewar sa, akwai hanyoyi da dama da za a magance satar mai ko kuma ladaftar da waɗanda gwamnatin ta ce su suke karkatar da tallafin man.

Misali, a cewar sa, hukumar Kwastam za ta iya sa ido a kan masu fita da man suna sayar da shi a ƙasashen ƙetare, ga hukumar EFCC da aka yi ta don binciken Laifuka, ga hukumar NSCDC da aka yi ta don kula da kayan gwamnati da sauransu.

Yanzu a cewar sa waɗancan hukumomi duk su kasa gano waye ya saci kaza ko ya fitar da kaza?

Don haka, a cewar sa, tallafin rage raɗaɗin ma ko rage raɗaɗin wucin-gadi ba ya yi ga al’umma ballantana a yi tunanin na din-din-din.

A shawarce a cewar sa, ya kamata gwamnati ta dawo da tallafin mai, domin tsadar man tana janyo talauci wanda yake ƙara hauhawar aikata laifuffuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *