‘Yan Arewa ba sa ƙiyayya da Kano

Daga MUS’AB MAFARA (PHD)

Wato wasu mutane sun ɗauka sharhin da a ke yi a Soshiyal midiya shi yake nuna matsayi da ra’ayin gama-garin al’umma a kan wani maudu’i da a ke tattaunawa a kai. Sannan wasu mutane kuma da zarar sun haɗu da maganar da ba ta yi mu su daɗi ba daga wasu mutune ‘yan kaɗan, sai su yi wa al’ummar da mutanen nan suka fito kuɗin-goro cewa duka ra’ayinsu kenan.

Kawai don ka ga, misali, kwamen 100 (in ma sun kai) na mutane da su ke sukar mutanen Kano ko su ke jin daɗin abun da ya faru da jam’iyyarka, ba dai-dai ba ne ka ce yawancin ‘yan gari kaza ko ma ‘yan sauran jihohin Arewa ba sa son Kano. Kai ma ka na yin irin kuskuren da waɗancan ke yi ne l na yi wa mutane jam’i.

Shi ɗankasuwa daga Bukkuyum ko Illela ko Jega ko Nguru ina ruwansa da wanda ke gwamna a Kano? In dai za a cigaba da kawo kaya Kwari ya je ya sara ya samu riba, ai shi Kano gare shi aljanna ce.

Ba za a rasa masu ƙin Kano har cikin zukatansu ba ko don saboda ƙyashi na ɗaukakar ta in ka kwatanta da sauran jihohin Arewa ko kuma saboda wata musgunawa da ya samu daga hannun Kanawa, ko kuma saboda wasu halaye na Kanawan da ya yi hulɗa da su da bai yi masa ba ko ma ba tare da wani dalili ba.

Amma wannan ana samu game da ko wane gari da kuma ko wace al’umma a duniya. Ka fahimci cewa, gwargwadon girma da muhimmancin gari a cikin al’umma gwargwadon yadda wannan al’ummar za ta sa ma sa ido, kuma gwargwadon yadda za su tofa albarkacin bakinsu in a na tattauna lamurran da suka shafi garin.

Yawancin ‘yan Arewa kam ko dai ba su damu da Kano ba gabaɗaya ba, saboda harkokin gabansu sun ishe su, ko kuma suna son garin saboda amfani da suke samu daga gare shi ta fuskar kasuwanci ko ilmi ko auratayya ko zumunta ko nishaɗi daga Kannywood ko sun ma ɗauki Kano ta zama garinsu na din-din-din.

Ko kuma ka samu wasu waɗanda su suna bibiyar lamurran Kano ne saboda zaman garin babbar cibiyar kasuwanci da siyasa da al’ada da ilmi a arewacin Nijeriya kuma ta zama wani ma’auni na fahimtar ya lamurra za su iya kasancewa a yankin arewar?

Ya kamata in qara da cewa, su ma masu game ‘yan Arewa da zagi ‘yan-cikon-cokali ne daga cikin mutanen Kano ma da su ke Soshiyal midiya balle ma gama-garin mutanen Kano. Mai yiwuwa ma wani ya ce bai cancanta a yi musu raddi ba saboda ƙarancinsu.

Sai dai ni na tsani duk wata magana da ke ƙoƙarin raba kan Musulmi da ɗaukar bambancin da bai kai ya kawo ba a kambama shi.

Yawancin mu ba a abun da ke tsakaninmu da mutanen Kano sai so da mutunta juna, da hulɗoɗi na kasuwanci da raha da auratayya da taimakekeniya.

Kada ka bari wani ya zuga ka ka ƙi ɗanuwan ka kawai don ya fito daga wata jiha. In ka yi haka ba ka da bambanci da wanda kullun ƙoƙarinsu shi ne raba Musulmin Hausa da Musulmin Fulani.

Koyaushe ka mu’amulanci mutane a kan ɗaiɗaikunsu. Za ka samu wawayen mutane da ke sakin maganganu daga ko ina a Arewa. Za ka samu mutane masu son haddasa gaba da ƙiyayya a ko’ina cikin arewa.

Amma hwa dut wanga bayani bai canza cewa Sakkwatawa su at gaba Kanawa na biye ba!

Musab mafara (PHD), mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum musamman ma dai na siyasa da zamantakewa.