‘Yan bindiga da dama sun miƙa wuya ga sojojin Nijeriya

Daga USMAN KAROFI

Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa wasu shugabannin ’yan bindiga da dama sun miƙa wuya ga dakarun soji a yankunan Arewa ta tsakiya.

A wata sanarwa da daraktan harkokin watsa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce fitattun ’yan bindigan da suka miƙa wuya sun haɗa da Yellow Jambros, Alhaji Mallam, Ardo Idi (Alhaji Lawal), Lawal Kwalba, Salkado, Yellow Ibrahim, Gana’e da Babangida. Ya ƙara da cewa wasu ’yan ta’addan sun nuna sha’awar miƙa wuya sakamakon hare-haren sojoji da kuma haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki don shawo kan su wajen miƙa wuya.

Janar Buba ya ce sojoji za su ci gaba da kai hare-hare don murƙushe sauran ’yan bindiga ko kuma su miƙa wuya. A cikin nasarorin da aka samu cikin mako guda, dakarun sun kashe ’yan ta’adda 135, sun kama mutane 185, sun ceto mutane 129 da aka yi garkuwa da su. A yankin Kudu maso Kudu, an hana satar mai da kuɗinsa ya kai naira miliyan 889.2.

Haka kuma, sojojin sun gano makamai 113 da alburusai 2,415, ciki har da bindigogi 72 kirar AK47, bindigogi na gida 15 da bama-bamai huɗu. Sun kuma lalata haramtattun matatan mai guda 82 da kuma gangunan mai kusan lita 909,800. Hakanan, an gano kekuna, wayoyi, da motoci waɗanda ake amfani da su wajen ayyukan ta’addanci.

Janar Buba ya bayyana cewa wannan nasarorin sun nuna jajircewar sojoji wajen daƙile ayyukan ta’addanci da satar mai a faɗin ƙasa, yana mai kira ga al’ummar ƙasa su ci gaba da bai wa sojoji goyon baya don samun cikakkiyar nasara.