’Yan bindiga sanye da hijabi sun hallaka ɗan sanda a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Da rana tsaka wasu mutane akan babur da ake kyautata zaton ɓarayin daji ne sun kashe wani jami’in ɗan sanda a ƙauyen Biyu na Ƙaramar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina yayin da ɗan sandan da sauran abokan aikinsa ke gudanar da aikin su a wani shinge na binciken ababen hawa.

Sun yi vadda kama a yayin da ɗaya daga cikin su na sanye da babbar riga ɗaya kuma ya saka hijabi.

Isar su wurin ke da wuya suka buɗe wa jami’in ɗan sandan wuta suka kuma kashe shi nan take suka kuma gudu da bindigar shi kamar yadda majiyar Manhaja ta tabbatar.

Tuni dai aka yi jana’izar Marigayi Ahmed Shu’aibu a Unguwar Kwaɗo dake cikin birnin Katsina.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ƙara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bada umarnin tabbatar da tsaron yankin tare da gano waɗanda suka yi aika-aikar.

Sai dai tun farko ‘yan bindigar dake aikin ta’addanci a yankin Batsari sun bai wa mazauna ƙaramar hukumar wa’adin mako guda inda suke neman a yi sulhu da su ko kuma su cigaba da kai wa al’ummar yankin hare-hare ba ƙaƙƙautawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *