‘Yan bindiga sun ɗauke amaryar da yaran Sarki a Kaduna

Wasu da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun kai hari fadar Sarkin Kagarko, Alhaji Sa’ad Abubakar, da ke yankin Kudancin Kaduna inda suka yi awon gaba da ahalin gidan da dama.

Waɗanda ‘yan bindigar suka sace sun haɗa da yara guda tara da jikoki da dama haɗi da wasu daga cikin garin.

Majiyarmu ta ce maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 11:15 na dare a ranar Lahadi inda suka tafi kai tsaye faɗar sarkin.

A cewar majiyar, “Sun ɗauke amaryar sarki tare da yara tara da kuma jikoki, amma amaryar ta samu ta kuɓuce ta dawo gida.”

Ta ƙara da cewa, “Maharan sun kashe wani makiyayi guda a ƙauyen Kuchimi, kana sun fasa shaguna bakwai a ƙauyen Janjala.”

Ya zuwa haɗa wannan labari, ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin ‘yan sandan Kaduna, DSP Muhammed Jalige, ya ci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *