’Yan bindiga sun aurar da ’yan mata 13 daga cikin ɗaliban Yauri

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Watanni 8 bayan da ‘yan bindiga suka yi awon gaba da ɗaliban sakandiren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta birnin Yauri a jihar Kebbi, har yanzu ‘yan bindigar suna riƙe da fiye da 10 daga cikinsu, duk kuwa da biyan kuɗin fansa da aka yi, da kuma musayar fursunoni da aka yi a lokuta daban-daban.

Wani bincike da jaridar ‘Daily Trust ta gudanar na nuni da cewa an aurar da kimanin ɗalibai  mata 13 ga ‘yan bindiga, kuma yanzu haka wasu daga cikinsu na da juna biyu.

A ranar 17 ga watan Yunin shekarar da ta gabata ne ɓarayin dajin da ke biyayya ga ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Dogo Gide  suka afka wa makarantar sakandiren Birnin Yauri a jihar Kebbi, inda suka yi awon-gaba da gwamman ɗalibai da malamai 5.

Binciken da jaridar ‘Daily Trust’ ta gudanar ya nuna cewa tsakanin ɗalibai 11 zuwa 14 na hannun ‘yan bindigar, kuma ɗaya ne kawai namiji daga cikinsu.

Wasu majiyoyi sun ce tabbas Dogo Gide ya aiwatar da barazanar da ya yi ta aurar da ‘yan matan da suka rage a hannunsa, inda yanzu haka wasu daga cikinsu na da juna biyu.

Wani wanda aka gudanar da tattaunawar sako ɗaliban Yaurin da shi, ya shaida wa jaridar ‘Daily Trust’ cewa  ko a tsakiyar watan Janairu an saki wasu ‘yan mata 3, amma da juna biyu suka dawo gun iyayensu.

Har yanzu gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce tana iya ƙoƙarinta na ganin an kuɓutar da ɗaliban da suka yi saura a hannun ‘yan bindiga.