‘Yan bindiga sun buƙaci fansar milyan N200 kafin su saki Sarkin Kajuru

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna

Kawo yanzu, ‘yan fashin dajin da suka yi garkuwa da Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, sun buƙaci a ba su fansar milyan N200 kafin su saki sarkin.

Idan dai za a iya tunawa, Manhaja ta ruwaito yadda aka sace basaraken tare da wasu ahalinsa su 13, ciki har da jikokinsa da safiyar Lahadin da ta gabata a gidansa da ke garin Kajuru a jihar Kaduna.

Mai magana da yawun Masarautar Kajuru, Dahiru Abubakar, shi ne ya bayyana batun kuɗin fansar da ‘yan bindigar suka nema a ranar Litinin.

Haka nan, Abubakar ya ce ‘yan bindigar sun ba da tabbacin cewa duka mutanen da ke hannunsu suna cikin ƙoshin lafiya babu wanda aka taɓa.

Daga nan, ya ce har yanzu masarautar Kajuru na roƙon ‘yan fashin dajin da su taimaka su sako sarkin mai shekara 85 da ma ahalinsa da ake riƙe da su ba tare da gidanya wani sharaɗi ba, musamman ma duba da lamarin lafiyar sarkin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *