‘Yan bindiga sun farmaki jirgin ƙasar Abuja-Kaduna

Daga BASHIR ISAH

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da harin cikin wata sanarwa da ya fitar a rana Litinin.

Kodayake dai Aruwan ya ce jami’an tsaaro sun yi nasarar kuɓutar da jirgin a ƙarshe.

A cewar Kwamishinan, “Jami’an tsaro sun sanar da Gwmnatin Jihar Kaduna cewa sojoji sun kuɓutar da jirgin da ya nufi Kaduna daga Abuja daga harin ‘yan ta’adda.

“Gwamnatin Kaduna ta sami rahotanni da dama a kan harin da ‘yan bindiga suka kai wa jirgin Abuja-Kaduna wanda ya auku a yankin Kateri-Rijana.”

Aruwan ya ci gaba da cewa, “gaggauta tura jam’ian tsaro zuwa yankin da lamarin yaa faru ya taimaka wajen kuɓutar da fasinjojin da ke cikin jirgin.

“Gwamnatin Jihar Kaduna za ta haɗa kai da Hukumar Kula da Jiragen Ƙasa (NRC) don tabbatar da adadin fasinjojin da ke cikin jirgin da kuma matsayinsu.

Tuni dai Gwamna Nasir El-Rufa’i ya jinjina wa jami’an tsaron bisa ƙoƙarin da suka yi wajen daƙile harin.

Harkokin ‘yan ta’adda tsakanin a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna sun sa matafiya da dama suka koma bin jirgin ƙasa wajen tafiye-tafiyensu.