‘Yan bindiga sun fille kan shugaban ƙaramar hukuma a Imo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu ‘yan bindiga a Jihar Imo da ke Kudu maso gabashin Nijeriya sun sare kan wani shugaban ƙaramar hukumar Ideato ta Arewa a jihar, bayan da suka sace shi a ranar Juma’ar da ta gabata.

‘Yan bindigar dai sun saki wasu hotunan bidiyo da ke nuna yadda suka ɗaure shugaban qaramar hukumar a hannaye, da kuma yadda suka halaka shi, bayan sun karvi kuɗin fansa don su sako shi.

Wata majiya a rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta jihar Imo, ta tabbatar wa BBC labarin kisan gillar da ‘yan bindigar suka yi wa shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Ideato ta Arewa a jihar, mai suna Chris Ohizu, qasa da kwana biyu da sace shi.

Majiyar ‘yan sandan ta ce, rundunarsu tana ƙoƙarin ceto shugaban ƙaramar hukumar daga hannun ‘yan bindigan da suka sace shi, sai kwatsam a daren Lahadi aka yi aune da wasu hotunan bidiyo da ke nuna yadda aka durƙusar da shi kan gwiwoyinsa, a wani ƙungurmin daji, aka ɗaure masa hannaye a harɗe ta baya, daga bisani kuma aka sare masa kai.

Amma dai rundunar ‘yan sandan ta bayar da tabbacin tana ci gaba da gudanar da bincike, har sai ta zaƙulo waɗanda ake zargi da tafka wannan aika-aika.

A ɗaya daga cikin hotunan bidiyon da suka karaɗe shafukan sada zumunta, da ‘yan bindigan suka saki, an ji wata murya tana barazanar halaka shi kansa gwamnan jihar ta Imo, Hope Uzodimma nan ba da daɗewa ba.

Muryar ta kuma ce, su ba ‘yan ƙungiyar tsaro ta ESN ko ƙungiyar ‘yan a-waren Biafra ta IPOB ba ne. Su dai gungun wasu mutane ne da ke fafutukar tabbatar da kafuwar jamhuriyyar Biafra a yankin Kudu maso gabashin Nijeriya, inda suka lashi takobin ba za su bari a gudanar da babban zaɓen da ke tafe ba.

Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka sace shugaban ƙaramar hukumar na riƙo, bayan sun harbe shi da bindiga a qafa, sannan suka banka wa gidansa wuta.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto dai gwamnatin jihar Imo ba ta ce uffa ba, game da aukuwar wannan lamari.