‘Yan bindiga sun halaka mutum 6, sun ƙona fadar sarki a Kogi

‘Yan bindiga a jihar Kogi sun halaka mutum shida tare da ƙona gidaje a harin da suka kai ƙauyen Bagana cikin ƙaramar hukumar Omala a safiyar Litinin da ra gabata.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar harin a jiya Laraba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Idrisu Dabban, shi ne ya tabbatar wa manema labarai da fauruwan haka bayan da ya ziyarci yankin da harin ya auku. Tare da cewa za a ɗauki matakin hana aukuwar hakan a gaba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa harin ya shafi fadar wani basarke Anyebe Salifu, mai daraja ta uku.

Bayanan shaidu sun ce, ‘yan bindigar sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 7 da rabi na safiyar rananar da lamarin ya auku bayan da galibin matasan yankin sun tafi gona inda suka tafi kai tsaye zuwa fadar sarkin.

Kazalika, an ce ɓatagarin sun banka wa fadar sakin wuta yayin harin tare da harbe mutum uku har lahira nan take.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *