Aƙalla ƙauyuka 23 da ke cikin ƙaramar hukumar Kontagora ta Jihar Neja sun rasa matsugunansu sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa yankin. Waɗannan ƙauyukan sun kasance kusa da filin horon sojoji da ke Kontagora.
Wakilin Kontagora II a Majalisar Dokokin Jihar, Abdullahi Isah, ya bayyana hakan yayin gabatar da ƙudirin gaggawa a zauren majalisar a zaman ta na ranar Talata. Ya ce filin horon sojojin aƙalla yana da faɗin daga Kontagora har zuwa wani ɓangare na Ƙaramar hukumar Mariga, inda mazauna yankin ke gudun hijira saboda yawan hare-haren ‘yan bindiga.
“’Yan bindiga sun kafa aƙalla sansanoni takwas a wannan yanki, wanda yanzu ya zama maɓoyarsu.
Wannan lamari ya haifar da babbar barazanar tsaro ga ƙauyukan da ke cikin Ƙananan hukumomin Kontagora da Mariga,” in ji Isah. Ya ƙara da cewa akwai wasu daga cikin mazauna waɗanda aka sace yayin hare-haren da har yanzu suna tsare a hannun ‘yan bindiga.
Majalisar dokokin Jihar Neja ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tuntuɓi hukumomin soji domin ƙara ƙoƙari wajen fatattakar ‘yan bindigar daga filin horon don mazauna yankin su samu damar komawa gidajensu.