‘Yan bindiga sun kashe ɗan takarar sanata a Inugu

Daga BASHIR ISAH

‘Yan sanda a Jihar Inugu sun tabbatar da ‘yan bindiga sun kashe ɗan takarar sanata na Jam’iyyar Labour a shiyyar Inugu ta Gabas, Oyibo Chukwu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Inugu, Daniel Ndukwu, ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis.

Ya ce lamarin ya faru ne ranar Laraba bayan da ‘yan bindigar suka yi wa motar marigayin kwanton-ɓauna suka banka mata wuta, kamar yadda jaridar News Point ta rawaito.

A cewar jami’in, “sun kai hari tare da ƙona motar kamfe ɗin Jam’iyyar Labour a Eke-Otu Amechi-Awkunanaw da ke Inugu, inda suka ƙona ɗan takarar sanata na jam’iyyar a Inugu ta Gabas, Barr. Oyibo Chukwu da hadiminsa da suke cikin motar tare har lahira.

“Amma jami’an tsaron sun daƙile ɓata-gari a lokacin da suka yi yinƙurin kai wa motocin tawagar ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar APC a jihar a ƙauyen Eke, Agbani, cikin Ƙaramar Hukumar Nkanu ta Yamma.”

Haka nan, ya ce an kuma kai wa mambobin Jam’iyyar PDP hari a yankin inda aka kashe wasu mambobin jam’iyyar.

Wannan na zuwa ne yayin da ya rage ‘yan sa’o’i kafin babban zaɓen 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *