‘Yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 50 a Giwa, Jihar Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan bindiga sun kai wasu manyan hare-hare kan ƙauyuka shida a Ƙaramar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna, inda suka kashe gwamman mutane a yankunan.

Gwamnatin Kaduna ta bakin Ma’aikatar Tsaro ta tabbatar da kai harin a ranakun Alhamis da Juma’a, amma ba ta bayyana adadin waɗanda aka kashe ba, tana mai cewa suna jiran cikakken rahoto kan lamarin.

Wasu rahotanni da Manhaja ta tattara a ta bakin yadda mutanen yankin ke bayyanawa, sun ce an kashe mutum kusan 50 tare da yin garkuwa da fiye da mutum hamsin.

Garuruwan da lamarin ya shafa sun haɗa da Dillalai, da Barebari, da Dokan Alhaji Ya’u, da Durumi, da Ƙaya da kuma Fatika.

Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ke shirin gangamin babban taronta a Abuja. Lamarin da ya sanya al’ummar yankin zargin shuwagabanni da nuna ko-in-kula ga al’ummar da suke shugabanta.

Amiru Lawal Balarabe, wani matashi ne mai fafutikar ganin an samu canji mai ma’ana a Ƙaramar Hukumar Giwa, ya nuna takaicin sa yadda ƙaramar hukumar ta zama yankin da ake kashe al’umma a ‘yan kwanakin nan.

A rubutun da ya yi a shafin sa na Facebook, yana cewa “wanda aka kashe bai san me ya yi aka kashe shi ba. Wanda ya yi kisan bai san abinda ya sa ya yi kisan ba.

Ya Allah ba wanda ya fi ƙarfin ka. Da mai kisan da masu ɗaukar nauyin su da ma waɗanda ya kamata su ɗauki mataki suka ƙi ɗauka,” a cewar sa.

Daga ƙarshe ya yi addu’ar Allah ya kawo wa al’ummar Ƙaramar Hukumar Giwa da Nijeriya ɗaukin gaggawa.

Ƙaramar Hukumar Giwa da ke a shiyyar Kaduna ta tsakiya ta kasance yankin da yake matuƙar fuskantar ƙalubalen tsaro, inda a ƙarshen shekarar bara ‘yan bindiga suka shiga wasu ƙauyuka suka hallaka sama da mutane 30 a rana guda, tare da jikkata wasu da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *