‘Yan bindiga sun kashe basarake da ‘ya’yansa huɗu a Kaduna

Daga WAKILINMU

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe Arɗon Birni da Kewaye na Masarautar Zazzau, wato Alhaji Shuaibu Mohammed tare kuma da wasu ‘ya’yansa huɗu.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar da daddare a ƙauyen Dorayi da ke Ƙaramar Hukumar Zaria, Jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar, ‘yan bindigar kimanin su biyar, sun kuma yi awon gaba da shanu 100 mallakar basaraken.

Matar marigayin, Malama Halima Shuaibu, ta faɗa wa manema labarai cewa maharan sun harbi magidan nata ne da bindiga a kai wanda hakan ya yi ajalinsa nan take.

Matar ta ce, “An fito da Arɗo waje daga ɗakinsa sannan aka harbe shi da bindiga a kansa sau biyu.

“’Yan bindigar sun shiga ɗaki-ɗaki a gidan inda suka kashe mini ‘ya’yana huɗu da suke da aure har da ‘ya’ya.

“Yaran da lamarin ya shafa su ne, Adamu Shuaibu, Musa Shuaibu, Abubakar Shuaibu da kuma Ibrahim Haruna.

“Bayan harin gidan, sun kuma kwashi shanu sama da 100,” in ji ta.

Wani ɗan Arɗon da ya tsira da ransa, Abdurrahman Shuaibu, ya ce maharan sun kuma kashe wasu mutum biyu a hanyarsu ta ficewa daga ƙauyen.