‘Yan bindiga sun kashe basarake, sun ƙona gidaje 50 a Binuwai

Daga BASHIR ISAH

Wasu ‘yan bindiga da ba a kai ga gano ko su wane ne ba sun kai wa yankin ƙaramar hukumar Oju na jihar Binuwai hari inda suka halaka sarkin ƙauyen Ochoro, Chief Okpe Denis Ijoko.

Bayanai sun nuna baya ga kashe Sarki Ijoko, ‘yan bindigar sun kuma ƙona gidaje sama da 50 tare da lalata ɗimbin dukiyoyi a ƙauyen a Ukpute yayin harin.


Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, da aka nemi jin ta bakin Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta ‘Yan Sandan Jihar, Anene Sewuese Catherine, ta ce labarin harin bai riga ya iso gabansu ba.

Amma wani babban malami a Jami’ar Jihar Binuwai kuma ɗan asalin ƙaramar hukumar da lamarin ya faru a cikinsa, Dr John Ogi, ya tabbatar da aukuwar harin ga jaridar DAILY POST.


Dr Ogi ya danganta harin da rikicin ƙabilancin da ke ci gaba da faruwa a tsakanin ƙabilara Tibi da Igede a yankin, yana mai cewa kimanin shekara guda kenan ana samun rashin jituwa a tsakanin ɓangarorin biyu.