’Yan bindiga sun kashe ladani a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari a cikin wani masallaci a Larabar da ta gabata a cikin garin Magazu a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, inda suka kashe ladani mai suna Abubakar Muhammad wanda aka fi sani da Abu Dogo ɗan shekara 25.

Wani mazaunin garin na Magazu mai suna Malam Isma’il Magazu a wata hira ta wayar tarho da Blueprint Manhaja ya ce ‘yan ta’addan sun kai hari masallacin ne da misalin ƙarfe 5:40 na safiyar ranar ta Laraba.

“Kamar yadda nake magana da kai yanzu, an yi jana’izar Marigayi Malam Abu Dogo kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau,” Malam Isma’il Magazu ya ce.

A cewarsa, ‘yanta’addar sun harbi marigayin har sau uku a ƙirjinsa a lokacin da yake gudanar da kiran sallar asubahi wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take.

Ya ce sun kuma yi garkuwa da wani Malam Ɗahiru Ya’u yayin harin, inda suka buƙaci a biya su Naira miliyan 10 a matsayin kuɗin fansa kafin su sake shi.

“Kamar yadda nake magana da kai yanzu, ‘yan bindigar sun sanar da mu cewar a biya su Naira miliyan goma a matsayin kuɗin fansa kafin su sako Malam Ɗahiru Ya’u da ke hannun su kafin su sake shi,” Malam Isma’il Magazu ya ce.

Malam Isma’il Magazu ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara da su ƙara ƙaimi tare da tura ƙarin jami’an tsaro ga al’ummar ƙaramar hukumar Tsafe da rashin tsaro ya shafa domin samar da zaman lafiya a yankin.

“Waɗannan ‘yan ta’adda sun addabi wasu al’ummomi da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Tsafe kusan kullum, don haka akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta ɗauki ƙwararan matakai don samar da tallafin tsaro domin dawo da zaman lafiya,” ya ƙara da cewa.

Haka zalika, jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, hanyar Funtuwa zuwa Gusau kusan sama da watanni biyu da suka shuɗe ta zama barazana ga masu ababen hawa sakamakon ayyukan ‘yan bindiga.

Sai dai ƙoƙarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Muhammad Shehu ya ci tura har zuwa lokacin da ake haɗa rahoton.