‘Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya da raunata bakwai a garin Gulma

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi

‘Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya sun raunata mutane bakwai a garin Gulma.
Kamar yadda waɗansu majiyoyi da abin ya faru a gaban su suka tabbatar, daren jiya Alhamis ne waɗansu ‘yan bindiga suka kai hari a garin Gulma da ke ƙaramar hukumar Argungu a Jihar Kebbi inda suka afka wani babban shagon sayar da kayan alatu da ake kira Aljazeera Supermarket mallakar wani ɗan kasuwa da a ke kira Alhaji Fatahu da misalin ƙarfe 9 na dare suka buɗe wuta.
Majiyar ta ce mutum ɗaya ya mutu kuma an harbi waɗansu mutane huɗu da ya gani da idonsa.

Wani ganau da bai so a bayyana sunan sa ba ya ce lokacin da mutanen garin suka ji harbe-harbe sai suka fito suka datse hanyoyi da makamai a hannu wanda ya yi sanadiyyar samun nasarar kwace babur ɗaya daga cikin baburan ɓarayin sai dai ɓarayin sun gudu, yanzu haka babur ɗin yana hannun ƴan banga.

Shugaban ƙaramar hukumar Argungu Honarabul Aliyu Sani Gulma ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce tuni tun lokacin da lamarin ya faru bai zauna ba har sai da aka ɗauki mutane bakwai da suka sami raunuka zuwa babbar asibitin tarayya (FMC) da ke garin Birnin Kebbi.
Uban ƙasar Gulma Alhaji Muhammad Bashar ya bayyana wa wakilinmu da cewa lokacin da abin ya faru yana Sokoto wajen wani aiki amma dai ya sami labari kuma ya yi addu’ar Allah ya jiƙan wanda ya rasu kuma ya baiwa waɗanda suka sami raunuka lafiya.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kebbi babban Sufurtandan ‘yan sanda Nafi’u Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce tuni an sanar da duk manyan jami’an tsaro na waɗannan sassan sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ya ce bai sami wani rahoto daga garesu ba.