‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda huɗu a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wasu ‘yan bindiga sun yi wa ‘yan sanda huɗu kwanton-ɓauna a hanyar Gusau zuwa Bunguɗu a Jihar Zamfara.

‘Yan sandan na aiki ne a ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Bunguɗu a lokacin da aka kai musu hari a daren ranar Litinin a jihar.

Wani shaida a yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa, an kashe huɗu daga cikin ‘yan sandan yayin harin

“’Yan bindiga da ke da yawan gaske sun kashe ‘yan sanda huɗu a Bunguɗu a daren jiya; sun yi wa ‘yan sandan kwanton-ɓauna ne a hanyar Gusau Bungudu kusa da kamfanin Nabature, sun kuma yi awon gaba da shanu da dama a ƙauyen Tagero da ke ƙarƙashin gundumar Furfuri a yankin Bunguɗu.”

An tattaro cewa ‘yan sandan sun ɗora shingayen binciken ababen hawa a hanyar Bunguɗu zuwa Gusau a lokacin da ‘yan bindigar suka yi musu kwanton-ɓauna suka buɗe musu wuta.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, ASP Yazeed Abubakar, ya tabbatar da faruwar harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *