‘Yan bindiga sun mamaye ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara da ke wakiltar, ƙaramar hukumar Anka, ya ce ‘yan bindiga sun mamaye akasarin mazaɓun da ke ƙaramar hukumarsa, lamarin da ya tilasta gomman al’umma neman mafaka zuwa wasu yankuna.

Hon Rilwanu Marafa Anka Na Gambo, ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da sashen Hausa na BBC, ya ce.

“Daga shekara 10 zuwa 20, ƙaramar hukumata ta Anka na fuskantar barazanar tsaro ƙwarai da gaske. Duk ƙauyukan cikin mazaɓu bakwai da nake da su a ƙaramar hukumar Anka kamar mazaɓar Waya, ‘yar Sabaya, Bageza, Sabon Birni duk ‘yan ta’adda sun mamaye. Haka kuma sauran mazaɓu duk sun mamaye.

Harwayau hedikwatar ƙaramar hukumar Anka ba su bar ta ba domin kwana huɗu da suka wuce sun je sun kwashe shanu, sun kwashe iyalan wasu,” in ji Hon Rilwanu.

Dangane kuma da yadda rayuwa take ga al’ummar yankin, Hon Rilwanu Marafah Na Gambo ya ƙara da cewa “babu daɗi halin da ake ciki sai dai Inna lillahi wa inna ilaihirrajiuun. Jama’a na cikin wahala da masifa da talauci. Hasali ma noma ba ya yiwuwa. Idan mutum ya kuskura ya yi tafiyar da ta wuce kilomita 50 daga cikin garin Anka to za ka kasance a hannun ‘yan bindiga.”