‘Yan bindiga sun sace ɗalibai mata kimanin 300 a Zamfara

Daga FATUHU MUSTAPHA

Rahotanni daga Jihar Zamfara, sun nuna cewa ‘yan bindiga sun sace ɗalibai mata kusan su 300 a Makarantar Sakandaren Gwamnati (GSS) Jangeɓe, da ke yankin ƙaramar hukumar Talata-Mafara a jihar, a tsakar daren Juma’a.

Kwamishinan Labarai na jihar, Malam Suleiman Tunau Anka, ya tabbatar wa manema labarai faruwar haka, inda ya ce ‘yan bindiga sun shiga makatar ne da misalin ƙarfe 1 na tsakar daren Juma’a suka kwashi ɗalibai.

Sai dai Anka bai faɗi adadin ɗaliban da lamarin ya shafa ba.

Wannan na faruwa a daidai lokacin da Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yaba wa gwamnatinsa bisa tsarin da ta ƙirƙiro na wanzar da zaman lafiya da tattaunawar sulhu da zummar daƙile matsalar ‘yan fashi da rashin tsaro.

Matawalle ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi wasu ‘yan fashin daji da suka tuba suka ajiye makamansu a Zamfara a rana Alhamis.

Yana mai cewa yana da yaƙinin wannan tsari da ya ƙirƙiro zai amfani ƙasa bakiɗaya ba jihar Zamfara kaɗai.

Gwamnan ya toge kan cewa ba duka Fulani ne ɓatagari ba, wasunsu sun shiga harkar aikata manyan laifuka ne ba dan sun so ba.

Makaman da tubabban ‘yan fashin suka miƙa sun haɗa da bindika ƙirar AK-47 guda bakwai da bindiga mai jigida guda 2, alburusai da sauransu.

Tun bayan samar da shirin nasa, Matawalle ya ce ana ci gaba da samun ‘yan bindigar da suka karɓi shirin, suka tuba tare da miƙa makamansu.