‘Yan bindiga sun sace amarya ana tsaka da biki a Neja

Daga BASHIR ISAH

A ranar Asabar da ta gabata ‘yan bindiga suka kai hari a ƙauyen Gbacitagi da kewaye a yankin ƙaramar hukumar Lavun a jihar Neja inda suka ɗauke amarya ana tsaka da bikin aure tare da halaka aƙalla mutum goma.

Rahotanni daga yankin sun ce ‘yan bindigar sun wawushe kayayyaki da kuɗaɗen da suka tarar a wajen bikin.

Maharan wanda aka ce adadinsu ya haura mutum 100 sun farmaki ƙauyukan yankin ne ɗauke da muggan makamai kuma a kan babura.

Haka nan, an ce ‘yan bidingar sun kwashi shanu da kayan abinci masu yawan gaske yayin harin.

Sauran ƙauyukan da harin ‘yan bindigar ya shafa sun haɗa Egbako, Ndaruka, Ebbo, Ndagbegi, Tshogi, Gogata, Ndakogitu Tsonfadagabi, Kanko da kuma Gbacitagi.

Bayanai sun ce maharan sun fuskanci cikas a ƙauyen Akere yayin da suka yi ƙoƙarin haye gadar da ta haɗa yankin da Wushishi kasancewar gadar ta karye. Lamarin da ya sa suka fuskanci tasgaro wajen ƙetarewa da shanun da suka sato wanda hakan ya sa a bisa tilasa suka bar shanun a nan sannan suka tsere.

Ya zuwa haɗa wannan labari, babu wani bayani kan amarya da kuma sauran mutanen da ‘yan bindigar suka kwashe.