‘Yan bindiga sun sace basarake a Filato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun sace wani basarake, Alhaji Dabo Gutus a ƙauyen Tal da ke Ƙaramar Hukumar Pankshin a Jihar Filato.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne misalin ƙarfe ɗaya na dare a ranar Litinin.

Wani mazaunin ƙauyen ya ce mutane na ta ƙoƙarin kiran ‘yan bindigar don sanin halin da basaraken yake ciki.

Prince Dakup Ezra, wanda yake wakiltar ƙauyen Panshin a majalisar dokoki, ya yi kira a kwantar da hankali, yana mai cewa babban burinsu shi ne a kuɓutar da basaraken, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Ya yi kira ga mazauna masarautar da kuma yankin baki ɗaya da su guji yin gaban kansu.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Filato, Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.