‘Yan bindiga sun sace hamshaƙin ɗan kasuwar Kano, sun harbi mutum biyu da bindiga

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da hamshaƙin ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Nasiru Na’ayya.

Bayanai sun nuna da tsakar daren Litinin ‘yan bindigar suka sace Na’ayya a Ƙauyen Gangarbi da ke yankin Ƙaramar Hukumar Rogo a Jihar Kano.

Wani ganau kuma ɗan uwan Na’ayya, wanda bai so a ambaci sunansa ba ya tabbatar da faruwar hakan.

Ya ce da tsakar daren Litinin ‘yan bindigar suka shiga gidan ɗan kasuwar, inda suka shiga harbin bindiga a iska don razanarwa.

“Yayin da mazauna yankin suka yi ƙoƙarin daƙile ‘yan bindigar daga barin wucewa da ɗan kasuwar, a nan suka harbe mutum biyu inda nan take ɗaya daga cikinsu ya mutu.

“Yayin da gudan ya ji rauni wanda a halin yanzu ana ci gaba da yi masa magani a asibiti,” in ji ganau ɗin.

Bayanai sun nuna a lokutan baya-bayan nan ƙauyen Gangarbi da maƙwabtansa na yawan fuskantar barazana daga ‘yan bindiga.

Kakakin ‘Yan Sanda a Kano, SP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da aukuwar lamarin, tare da cewa yana jiran cikakken bayani kan batun daga DPO na yankin kafin shi ma ya yi wa al’umma bayani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *