‘Yan bindiga sun sace jami’ar Shirin Ƙidaya, sun nemi a biya fansar N500m

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Kwamishinar Tarayya mai wakiltar Jihar Bayelsa a Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa, Mrs Gloria Izonfuo.

Majiyarmu ta ce an sace Gloria ne da yammacin Lahadi a yankin mararrabar Ogbakiri cikin Ƙaramar Hukumar Emohua a Jihar Ribas.

Bayanai sun ce Kwamishinar na kan hanyarta ta zuwa Fatakwal, Babban Birnin Jihar Ribas, bayan ta baro Ƙaramar Hukumar Brass da ke Jihar Bayelsa.

An ce ‘yan bindigar sun tsare motarta ne a kan babbar hanyar yanki inda suka yi awon gaba da ita tare da direbanta.

Haka nan, an rawaito cewar ‘yan bindigar sun buƙaci a biya su fansar Naira miliyan 500 kafin su sako Kwamisjinar da direban nata.

Kakakin ‘Yan Sanda Jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar hakan.

Ta ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ba da odar a tura jami’ai don su bi sawun ɓarayin don su kuɓutar da waɗanda lamarin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *