‘Yan bindiga sun sace mahaifiyar ɗan majalisa a Kano

Daga WAKILINMU

Bayanan da MANHAJA ta samu daga jigar Kano,sun nuna wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun dira Kano har ma sun sace mahaifiyar ɗan Majalisar Jihar mai wakiltar Mazaɓar Gezawa, Hon. Isyaku Ali-Danja.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta kalato cewa, ‘yan bindigar sun yi dirar mikiya ne a gidan mahaifiyar ɗan majalisar da ke Gewaza da misalin ƙarfe ɗaya na dare inda suka fasa ƙofar gidan da ƙarfin tsiya kana suka yi awon gaba da dattijiyar.

Da yake bayani kan lamarin, Ali-Danja, wanda tsohon shugaban majalisar Kano ne, ya ce da farko sai da ‘yan bindigar suka buƙaci mahaifiyar tasa ta buɗe musu ƙofa don su shiga amma ta ƙi ba su haɗin kai wanda a sakamakon haka ne suka fasa ƙofar da ƙarfi suka shiga ɗakinta suka ɗauke ta.

Ya ci gaba da cewa, jim kaɗan bayan harin ne sai ɗaya daga cikin hadiman dattijiyar ta yi yekuwa kana aka sanar da ‘yan snada.

A cewarsa, “Tun kafin na isa Gezawa DPO na yankin ya kira ni ya shaida mini cewa tuni an tura jamiai wurin da lamarin ya faru har ma an soma gudanar da bincike”.

Ya zuwa haɗa wannan rahoto, Ali-Danja ya ce ‘yan bindigar ba su tuntuɓe shi ko wani ahalinsu ba tukuna balle ya san abin da suke buƙata. Tare da cewa, suna addu’ar Allah Ya ceci mahaifiyar tasu daga hannun ‘yan ta’addan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *