‘Yan bindiga sun sace masu yi wa ƙasa hidima a Ribas

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga sun sace wasu masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) a kan hanyarsu ta zuwa Fatakwal bayan sun sallami sansanin ‘yan yi wa ƙasa hidima a Jihar Ondo.

Rahotanni daga yankin sun ce, waɗanda lamarin ya shafa wanda ba a tantance yawansu ba, an yi garkuwa da su ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 9 na dare.

Wani ganau wanda ‘yar uwarsa na daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin, ya tabbatar wa wani gidan rediyon Fatakwal faruwar hakan a ranar Laraba.

Ya ce lamarin ya auku ne a yankin Rumuji cikin Ƙaramar Hukumar Emohua, Jihar Ribas.

Ya ƙara da cewa, biyar daga cikin masu yi wa ƙasa hidimar sun samu sun tsere inda suka kai rahoton abin da ya faru ofishin ‘yan sanda na yankin Rumuji.

Ita ma Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ribas ta tabbatar da aukuwar hakan.

Kakakin rundunar, SP Grace Iringe-Koko, ta ce an kuɓutar da wasu daga cikin waɗanda aka sacen, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ganin yadda za a kuɓutar da sauran.