‘Yan bindiga sun sace mutane 29 a ƙauyen Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu mutane 29 da suka haɗa da manya maza, matan aure da yara a ƙauyen Yewuti, mahaifar tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Kwali, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti.

An samu labarin cewa wasu matan aure biyu, Zainab Umar da Aisha Zubairu, sun tsere daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da su a lokacin da aka kai su cikin daji.

Daga cikin waɗanda aka sace akwai Idris Mohammed, Abdullahi Zubairu, Sani S. Magani, Peter Modu, Ibrahim Mamman, Yellow Abdulrasheed, Musa Suleiman, Simbiya Ishaku, Sumaiya Ibrahim, Muktari Yunusa da Mohammed Yeluwa da Rahmat Shagari.

Sauran waɗanda abin ya shafa sun haxa da, Sumaiya Abubakar Yelwa, Mohammed Yelwa, Maimuna Muhammad, Hussaini Ya Nda Agyana, Hamza Ibrahim, Lantana Yunusa, Nabila Agyana, Rufai Salihu, Nafisa Aminu, Kasimu Adamu, Abako Adamu, Abdulyakin Aliyu, Lukman Aliyu, Rahina Audu, Abdulrazak Usman, Sadiya Usman, Darius Samuel da Japheth Osu.

Wani mazaunin garin Yewuti, wanda ya tsere, Shuaibu Ndako, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a lokacin da wakilinmu ya ziyarci yankin a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Talata, inda masu garkuwa da mutane da yawa suka mamaye al’ummar.

Ya ce masu garkuwa da mutanen da suka raba kan su rukuni-rukuni, sun je gidaje takwas ne a yayin da suke ta harbe-harbe, inda suka tafi da mazauna yankin ciki har da yara da matan aure cikin daji.

“Allah ne ya cece ni. Da na fara jin an buga min ƙofa, na leqo ta taga na ga masu garkuwa da mutane ne. Don haka na vuya,” inji shi.

Ya ce an yi garkuwa da yara biyu da mata biyu a gidansa kafin masu garkuwan su wuce gida na gaba bayan sun buɗe ƙofar gidan ta ƙarfin tsiya.

Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti, wanda ya zanta da wakilinmu a ƙauyen, ya ce an yi garkuwa da ƙaninsa Idris da matan yayansa guda biyu da wani yaro a gidansu.

Ya ce masu garkuwa da mutanen da suka yi aiki daga ƙarfe 1 na dare zuwa qarfe 3 na dare, sun mamaye gidaje sama da takwas sannan suka yi awon gaba da mutane 29 da suka haɗa da mata da maza da yara.

Ya ce wasu matan aure biyu sun yi nasarar tserewa daga hannun waɗanda suka sace su yayin da aka kai su da sauran waɗanda abin ya shafa cikin daji.

Shi ma Etsu Abawa na Yewuti, Alhaji Isyaku Yakubu Yewuti, ya tabbatar da cewa an yi awon gaba da mutanensa 29.

Ya ce an kai mutane biyu da suka samu raunukan harbin bindiga zuwa wani asibiti mai zaman kansa da ke Kwali.

Sarkin wanda ya ce ɗaukacin al’ummar yankin sun firgita da harbin bindiga da masu garkuwa da mutanen ke yi a lokaci-lokaci, ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da abin ya shafa da su taimaka masa wajen ceto waɗanda aka sace.

Mutanen ƙauyen Awawa da ke makwabtaka da garin Abaji da Wako suka shiga cikin jama’a don jajantawa iyalan waɗanda aka sace.

An kuma ga mafarauta, ‘yan banga, da ‘yan sanda a cikin motocin ƙirar Hilux guda uku suna shawagi a dajin ƙauyen.

Kawo yanzu dai babu wani martani a hukumance daga kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine, kan sabon harin da aka yi na garkuwa da mutane har zuwa lokacin haɗa rahoton.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *