‘Yan bindiga sun sace wasu ɗalibai a Delta

Daga BASHIR ISAH

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu ɗalibai da ba a san adadinsu ba a Jihar Delta.

Lamarin ya faru ne a ranar Litini a lokacin da ɗaliban ke kan hanyarsu ta tafiya a yankin Ughelli da ke jihar.

Duk da dai babu wani cikakken bayani kan batu, sai dai Kakakin ‘yan sandan jihar, Bright Edafe, ya ce jami’an tsaro sun samu lamrin aukuwar lamarin.

Jami’in ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Rundunar ‘yan sanda jihar ta samu labarin aukuwar wannan mummunan al’amari, kuma muna bakin ƙoƙarinmu don kuɓutar da su ba tare da ko ƙwarzane ba.”

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da wasu ɗalibai uku daga Jami’ar Calabar (UNICAL), Jihar Cross River.