‘Yan bindiga sun sace wasu ɗaliban jami’ar FUDMA a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu mutane ɗauke da bindigogi da ake kyautata zaton ɓarayin daji ne sun sace ɗalibai mata biyar dake karatu a Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutsinma, wato FUDMA dake Jihar Katsina.

‘Yan bindigar sun kutsa kai a gidan da ɗaliban ke kwana wanda ke wajen jami’ar bayan makarantar Mariamoh Ajiri dake garin na Dutsinma.

Majiyar Manhaja ta ce ‘yan bindigar sun yi dirar mikiya a rukunin gidajen da ɗaliban suka kama haya da misalin karfe 2:30 na safiyar Talata zuwa wayewar garin Laraba.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda na jihar Katsina, ASP Sadiq Abubakar ya tabbatar da sace ɗaliban.

Ta bakin Kakakinta, Rundunar ta bayyana cewar, an kama mutum ɗaya da ake zargi da ba wa ɓarayin dajin bayanan sirri, sannan an kama wasu mutane da dama da ake zargi da hannu a sace ɗaliban.

ASP Abubakar ya ƙara da cewa, Rundunar na ci gaba da gudanar da bincike tare da tsaurara tsaro don ceto ɗaliban da sauran mutane da ‘yan ta’addar ke tsare da su.

Lamarin na zuwa ne ƙasa da makonni biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka shiga jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau Jihar Zamfara, inda suka sace ɗalibai mata fiye da 40, sai dai daga baya jami’ar ta tabbatar da sakin wasu daga cikin su.