’Yan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai mata a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu gungun ’yan ta’adda sun sace ɗalibai mata biyu na Jami’ar Tarayya da ke Gusau (FUGUS) a Jihar Zamfara.

An ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi 2 Afirilu, 2023 lokacin da ’yan ta’addan suka farmaki ɗakin kwanan ɗaliban da ke Sabon-Gida.

Rahotanni sun ce, ’yan matan da aka sacen sun haɗa da wata mai suna Maryam da kuma Zainab.

’Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, inda Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Mohammed Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya bayyana yadda ya faru.

A cewarsa, ’yan ta’addan sun mamaye ɗakin kwanan ɗaliban ne da ke ƙauyen Sabon-gida a Ƙaramar Hukumar Bungudu da ke jihar ta Arewa maso Yamma.

A lokacin da su ke ɓarnar, an ce sun ɗaure masu gadin gidan ɗaliban, inda suka kwace wayoyinsu kafin tafiya da ɗaliban da ke karatun ilimin ƙananan ƙwayoyin halittu (Microbiology).

A cewar kakakin, “A lokacin da muka samu rahoto, rundunar ’yan sanda ta gaggauta zuwa wurin, amma aka tarar har ’yan ta’addan sun tsere da waɗanda suka sacen zuwa wani wuri.

“Kwanishinan ’yan sanda daga baya ya tura jami’ai domin aikin ceto waɗanda aka sacen cikin ƙoshin lafiya, tare da kamo waɗanda suka yi ɓarnar da kuma gurfanar da su a gaban koliya.”

Kakakin ya ƙara da cewa, kwamishina Kolo Yusuf ya buƙaci mazauna da su kwantar da hankali tare da bai w ’yan sanda haɗin kai a ƙoƙarinsu na ceto ’yan matan cikin ƙoshin lafiya.