’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane fiye da 10 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu mutane da ake kyautata zaton ɓarayin daji ne sun yi awon gaba da kimanin mutum 11 akasarinsu mata da ƙananan yara a ƙauyen Shimfiɗa dake a ƙaramar hukumar Jibiya ta jihar Katsina a lokacin da mutanen  ke ƙoƙarin tserewa daga garin don isa tudun mun tsira.

Mafi akasarin waɗanda aka yi garkuwar da su tsofaffin mata ne da ba su samu damar  tserewa a ranar Alhamis ɗin makon jiya, bayan da sauran mazauna garin su ka bar garin sakamakon tsoro da fargabar abun da ka je ka dawo na hare-haren ‘yan bindiga.

Idan za a iya tunawa Manhaja ta kawo labarin yadda wasu ƙananan yara guda bakwai su ka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin da aka samu a garin na Shimfiɗa bayan da hukumomi su ka janye sojojin dake samar da tsaro a yankin inda mazauna garin suka firgice su ka kuma yanke shawarar yin gudun hijara zuwa garuruwan da ke maƙotaka da su saboda a cewar wani mazaunin garin da ya zanta da Manhaja ɓarayin za su iya kawo wa garin hari a kowane lokaci tun da sun san  ba bu jami’an tsaro.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai a yayin wata ganawa a hedikwatar rundunar dake birnin Katsina kakakinta SP Isa ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya buƙaci al’umma da su daina ɗaukar jita-jita akan batun.

Ya bayyana cewar har yanzu ‘yan sanda da sojoji su na gudanar da ayyukansu a yankin.

Ya kuma bayyana cewar kwamishinan ‘yan sandan jihar, Idris Dauda Dabban ya umarci babban kwamandan ‘yan sandan kwantar da tarzoma wato akan ya tabbatar an samar da tsaro a yankin.

SP Isa ya kuma tabbatar wa mazauna garin cewar su kwantar da hankalinsu jami’an tsaro ba su bar yankin ba saboda a cewar sa mutane ne ke yaɗa jita-jitar hakan.

“Mutane su na son yaɗa jita-jita wanda hakan bai da ce ba idan abu makamancin haka ya faru bai kamata mutane su dinga faɗar duk abunda ya zo mu su a baki ba wanda hakan shine ya haddasa turmutsitsi a garin,” inji shi.

Daga ƙarshe ya tabbatar wa mazauna garin cewar har yanzu akwai jami’an tsaro a yankin kuma za su ci gaba da samar ma su da  tsaro.