‘Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon ɗan majalisar Kogi a Abuja

Daga WAKILINMU

Da sanyin safiyar Alhamis wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka sace tsohon ɗan Majalisar Dokoki na jihar Kogi, Friday Sani Makama, a wani otel da ke Abuja.

Ɓarayin sun kai wa ɗan majalisar hari ne ɗauke da bindigogi a ƙauyen Tugun Mada da ke yankin Zuɓa a Abuja, inda suka yi harbe-harben bindiga a iska don razanar da jami’an tsaron da ke kusa.

Makama ya taɓa wakiltar mazaɓar Igalamela Odolu a Majalisar Dokokin jihar ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Bayanai sun nuna iyalan Makama sun samu sanin halin da ya faɗa ciki ne bayan da manajan otel ɗin, Mr Adejoh Maquile, ya kira ɗaya daga cikin ahalin ɗan majalisar mai suna Prince Frederick Adejoh (Oma Onu Aya) da sauransu inda ya shaida musu cikin murya mai karkarwa cewa an yi garkuwa da su ne.

Wato dai ‘yan bindigar sun haɗa da manajan otel ɗin tare da ɗan majalisar suka yi gaba da su.

Ya zuwa haɗa wannan labari, ba a kai ga tantancewa ‘yan bindigar, shin masu garkuwa da mutane ne don neman kuɗin fansa ko kuwa a’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *