‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawaƙi Rarara

Daga Umar Garba a Katsina

Wasu ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun afka gidan hajiya Halima Adamu, mahaifiyar fitaccen mawaƙin siyasar nan Dauda Adamu Kahuru Rarara a gidanta dake Kahutu a ƙaramar hukumar Ɗanja ta jihar Katsina.

Rahotanni da Blueprint Manhaja ta samu na nuna cewar ‘yan bindigar sun yi dirar mikiya a gidan hajiya Halima da misalin ƙarfe 1:30 na tsakar dare.

Mazauna garin da lamarin ya faru a gabansu sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa,

 “A kafa suka zo, kuma kasancewar ba su yi harbi ba a lokacin da suka kai harin sun yi garkuwa da ita cikin ’yan mintoci.

“Dattijuwar ba ta yi musu turjiya ba  a lokacin da suka ce ta biyo su.

“Duk da cewa ’yan bindigar sun samu wasu mutane a gidan, mahaifiyar Rarara kaɗai suka ɗauka.

“Babu wani yunƙuri da aka yi na tunkarar ’yan bindigar a lokacin da suke tafiya da ita saboda suna ɗauke da bindigogi,” in ji wani mazaunin ƙauyen na Kahutu.

Ya ce, “Watakila sun bar baburansu ne daga nesa suka taka zuwa cikin ƙauyen.

“Muna rokon Allah Ya kubutar da ita cikin ƙoshin lafiya, domin tana taimaka mana sosai a wannan ƙauyen.

“Ɗanta Rarara mai yawan taimakon al’umma ne, kuma ya kawo mana abubuwan cigaba sosai a garinmu,” in ji shi.

Har zuwa haɗa wannan rahoto Rarara bai fitar da wata sanarwa ba game da lamarin kazalika, yunƙurin da Manhaja ta yi na tuntuɓar  ma su taimaka masa kan yaɗa labarai ya ci tura.