‘Yan bindiga sun yi garkuwa da uba da ɗansa a Abuja

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun sace wani magidanci mai suna Abdullahi Benda tare da matashin ɗansa, Jibrin Abdullahi Benda, a ƙauyen Yangoji da ke yankin hukumar Kwali a Abuja.

Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa, wannan al’amari ya faru ne da safiyar jiya Juma’a.

Bayanan mazauna yankin su nuna cewa, ɓarayin sun haura ta katanga ne suka samu shiga gidan da suka sace waɗanda lamarin ya shafa.

Haka nan, an ce ‘yan fashin sun yi harbe-harben bindiga a iska don tsorata jama’ar yankin.

An ce bayan da suka samu shiga gidan, sai suka fasa ƙofar ɗaki da ƙarfin tsiya inda suka shiga suka ɗauki magidancin da ɗansa ta hanyar nuna musu bindiga.

Bayanai sun nuna ‘yan bindigar sun yi yunƙurin tafiya da matar gidan amma sai suka bar ta albarkacin renon goyon da take da shi.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Birnin Tarayya, ASP Daniel Y. Ndiparya, ya tabbatar da aukuwar lamarin, tare da cewa tuni sun baza jami’ai don kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwan da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *