
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Jihar Katsina ta ce, mahaddacin Al-ƙur’ani, Abdussalam Rabi’u Faskari da mahaifinsa da ɗan uwansa suna raye, amma a hannun ƴan bindigar da suka yi garkuwa da su.
Kwamishinan Labarai da Al’adu na jihar, Dakta Bala Salisu Zango ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Asabar.
Kwanaki biyu da suka gabata ne aka yi garkuwa da su akan hanyarsu ta zuwa Faskari daga cikin garin Katsina bayan amsar gayyatar Gwamna Dikko Raɗɗa na ƙoƙarin da mahaddacin yayi a yayin musabaƙar da ta gabata.
Kwamishinan ya ce, mahaddacin zai wakilci Nijeriya ne a gasar musabaƙa ta Ƙasa-da-ƙasa da ke tafe.
Hakan ya biyo bayan saƙonnin jajaje da ta’aziyya ne da aka yi ta aika wa gwamnatin jihar daga wurare da dama waɗanda daga ciki akwai na gwamnatin Jihar Kebbi, sakamakon yaɗa batun mutuwar mahaddacin a hannun ƴan bindiga, inda suka yi godiya game da hakan.
Ya ƙara da cewa, yayin da suka tabbatar da yin garkuwa da mutane ukun, haka kuma suna nan cikin ƙoshin lafiya a hannun ƴan bindigar.
A ranar Juma’a ne waɗanda suka yi garkuwa da su suka nemi iyalansu da su biya Naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa.
Ya kuma ce, Gwamna Raɗɗa ya koka kan faruwar abin alhinin, ya na mai masu addu’ar sake samun ƴanci.