Daga UMAR GARBA a Katsina
‘Yan bindinga dake garkuwa da tsohon daraktan hukumar yi wa ƙasa hidima (NYSC) Janar Maharazu Tsiga mai ritaya, sun buƙaci a biya su kuɗin fansa Naira miliyan 250 kafin su sake shi.
Ɗaya daga cikin makusantan Tsiga da ya buƙaci a sakaya sunansa ne ya bayyana haka a ranar Asabar da ta gabata.
Wani makusancin tsohon shugaban hukumar ta NYSC ya bayyana wa majiyar Blueprint Manhaja cewa shugaban ‘yan bindingar ne ya tuntuɓi iyalan Janar Tsiga mai ritaya a daren ranar Juma’a da ta gabata, inda suka kafa sharaɗin cewa sai an biya su kuɗi Naira milyan 250 kafin sakinsa.
Manhaja ta rawaito cewa an yi garkuwa da Tsiga tare da wasu mazauna ƙauyen Tsiga dake ƙaramar hukumar Ƙanqara a Jihar Katsina.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ‘yan bindinga dake ɗauke da muggan makamai sun raunta aƙalla mutane biyu tare da kashe wani abokin ta’addancinsu bisa kuskure a lokacin da suka kai harin a ƙauyen.
Tun a ranar Juma’a da ta gabata rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta tabbatar da yin garkuwa da Janar Tsiga mai ritaya, kakakin rundunar Abubakar Sadiq ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggauwar kai ɗauki a ƙauyen don ceto mutanen, sai dai a lokacin da suka isa wurin tuni ‘yan bindingar sun tsere da mutanen.
“Abin takaici, kafin isowar jami’an tsaron, ‘yan bindigar sun riga sun yi nasara a aikinsu.” In ji kakakin.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu rundunar na aiki ba dare ba rana tare da sauran jami’an tsaro dake jihar don ganin an ceto tsohon shugaban hukumar ta NYSC tare da sauran mutanen da ‘yan bindingar ke garkuwa da su.