‘Yan binga 20 sun baƙunci lahira bayan da suka yi yunƙurin shiga NDA

Daga BASHIR ISAH

Sama da ‘yan bindiga ashirin ne suka baƙunci lahira sakamakon artabun da suka yi da sojojin saman Nijeriya na rundunar ‘Thunder Strike’ a daidai lokacin da suka doshi makarantar bai wa sojoji horo, NDA a taƙaice ke Kaduna.

Sahihan majiyoyi sun shaida wa jaridar PRNigeria cewa, an ga ‘yan bindigar a ranar Alhamis da ta gabata a kan babura sama da guda 50 inda suka doshi NDA da ke Kaduna.

Idan za a iya tunawa, ‘yan bindigar sun samu nasarar kai hari cikin NDA a watan Yunin bara tare da sace wani babban soja kana suka bindige jami’ai biyu har lahira.

An ce sakmakon bayanan sirrin da sojojin suka samu game da zirga-zirgar ‘yan bindigar a yankin makarantar, ya sa aka tura jiragen yaƙi masu saukar ungulu guda biyu suka fatattake su.

Bayanai sun nuna ‘yan bindigar sun taso ne daga ƙauyen Damari da ke yankin Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna.

Sojoji sun ce bayanan da suka tattara bayan artabun sun nuna an yi nasarar yin maganin ‘yan bindigar yadda ya kamata wanda har an samu kashe kimanin mutum 20 daga cikinsu.

Haka nan cewa, sun tarwatsa shirin ‘yan bindigar na neman kutsawa NDA.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *