’Yan daba sun kashe mutum, sun jikkata wasu a wuraren zaɓe a Legas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mutum ɗaya ya rasa ransa, wasu da dama sun samu raunuka bayan da ’yan daba suka kai farmaki a rumufunan zaɓe a sassan Jihar Legas.

An gano cewa an bindige mutum ɗaya har lahira, wasu da dama kuma sun jikkata a lokacin da ɓata-garin suka yi dirar mikiya a wuraren zaɓen.

Yankunan da aka kai hare-haren sun haɗa da Ikota, Jakande, Ijegun, Festac da kuma Isolo.

Rikicin ya fara ɓarkewa ne bayan ɓata-garin sun kutsa cikin yankin Okota, inda jam’iyyar LP ke da ƙarfi.

Maharan sun fatattaki mutanen da suka fito yin kaɗa ƙuri’a, sannan suka lalata akwatunan zaɓe, suka tafi da wasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *