Da safiyar Aasabar wasu ‘yan daba suka tarwatsa kayan zaɓe a Gundumar Akati cikin Ƙaramar Hukumar Donga, Jihar Taraba.
Bayanai daga yankin sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da jami’an INEC ke ƙoƙarin raba kayan zaɓe zuwa rumfunan zaɓen yankin.
Wakilinmu ya ce tada ƙayar bayan ya yi sanadiyar jama’ar yankin kowa ya tsere don neman mafaka.
Wani ganau, Jame Chimi, ya ce zuwan sojoji ne ya taimaka wajen lafar da ƙurar da ‘yan dabar suka tayar.