’Yan damfara na karɓar bashin banki da lambar wayar ’yan sanda

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya gargaɗi ’yan Nijeriya da su daina amfani da lambobin gaggawa na ’yan sanda wajen karɓar bashi daga bankuna da sauran kamfanonin ba da bashi.

Egbetokun ya yi wannan gargaɗin ne ta wata sanarwa da kwamishinan ’yan sanda a babban birnin tarayya (FCT), CP Haruna G. Garba ya fitar a ranar Juma’a 28 ga watan Yuli, 2023.

Ya bayyana cewa, wasu mutane na amfani da layukan gaggawa cin bashin kamfanonin ba da bashi da ruwa.

“CP ta umurci mutanen da ke shigar da layukan gaggawa na ’yan sanda a cikin mugayen ayyukansu, da nufin yaudarar jama’a da waɗanda suka miƙa kai don samun lamuni su ƙaurace wa irin waɗannan ayyuka, domin su na amfani da layukan gaggawar ne kawai don manufar su. Hukumar za ta ɗauki matakin kamawa tare da gurfanar da masu aikata waɗannan laifuka,” in ji shi.

Bugu da ƙari, CP xin ya qaryata wani rahoto da ya yi ikirarin cewa masu garkuwa da mutane sanye da kakin ‘yan sanda sun yi awon gaba da wasu mutane 17 a unguwar Apo da ke Abuja.

Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya yana sanar da jama’a cewa savanin yadda ake yaɗa labaran qarya a kafafen yaɗa labarai na cewa masu garkuwa da mutane sanye da kakin ’yan sanda suna aikata miyagun ayyukansu kuma sun yi garkuwa da mutane 17 daga Unguwar Apo a Abuja, wani labari ne na ƙarya domin babu wani abu irib haka da ya faru a cikin FCT,” sanarwar ta fayyace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *