Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da suka yi ritaya a Kaduna, Kano, da Katsina, sun bayyana matuƙar ɓacin ransu kan jinkirin da aka samu wajen biyansu hakkokinsu na ritaya, wanda ke ƙara dagula musu rayuwa sakamakon ƙalubalen tattalin arzikin Nijeriya.
Yawancin masu ritaya, waɗanda wasu daga cikinsu sun bar aiki har zuwa Maris 2023, sun ba da rahoton cewa har yanzu suna jiran a fara buyansu kuɗin fansho.
A Kaduna, Ahmad Kawure, wanda tsohon ma’aikaci ne a hukumar kula da ayyukan yi ta ƙasa, ya bayyana rashin jin daɗinsa bayan ya shafe kusan shekara guda yana jiran kuɗin fansho wanda har yanzu ba a biya shi ba.
Kawure ya ce, “har yanzu ma’ajin kuɗin fansho na bai yi min bayani kan dalilin da ya sa aka samu jinkirin ba, amma mun ji hakan ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan hukumar fansho ta ƙasa (PENCOM) albashi,” in ji Kawure.
Ya ƙara da cewa, dole ne waɗanda suka yi ritaya su jira PENCOM ta biya kuɗaɗe ga masu kula da fansho kafin kowane biyan kuɗi ya isa gare su.
Ba a bayyana sunansa ba, wani mai ritaya na tarayya a Kaduna ya soki tsarin gwamnati, yana mai jaddada cewa mutanen da suka sadaukar da shekaru 35 a aikin gwamnati sun cancanci kulawa cikin lokaci da mutuntawa.
Ya ba da shawarar a tura kuɗaɗen fansho da aka tara zuwa PENCOM gabanin kwanakin ficewa daga masu ritaya don hana irin wannan jinkiri.
“Yawancin waɗanda suka yi ritaya ba su da gidajen kansu kuma suna dogara da tanadin ritaya ne don samun gidaje ko fara kasuwanci,” in ji shi.
“Ya kamata gwamnati ta ba da fifikon biyan kuɗi a kan lokaci don tallafa wa waɗannan mutanen da suka ba da shekarun aikin su ga aikin gwamnati.”
A jihar Kano, masu ritayar jiha da na tarayya na fuskantar irin wannan ƙalubale, inda ake samun tsaikon biyan fansho da kuma kuɗaɗen da ake biya a kowane, wanda ke ƙara taɓarɓara harkokin kuɗi.
Wani mai ritaya, Baba Isa, ya bayyana cewa, duk da kammala takardun da ake buƙata, har yanzu bai samu ko sisi daga shugaban asusun fansho (PFA) ba.
“Rayuwa ba za ta yiwu ba tare da kwanciyar hankali ba, tun lokacin da na yi ritaya ban samu sisi ba, abin da na tanada yana da ƙarewa,” in ji shi.
Wani mai ritaya, Adamu Aminu, ya bayyana yadda jinkirin ya ƙara ta’azzara yanayin lafiyarsa, saboda ba ya iya sayen magunguna masu muhimmanci.
“Ina roƙon PFA da ta saki fansho na – ya wuce shekara guda yanzu,” in ji shi.
Salisu Nura, wani mai ritaya, ya yi kira ga shugaban ƙƙsa Bola Tinubu da ya magance matsalar, inda ya jaddada yadda ƙarin farashin man fetur da hauhawar farashin kayayyaki ke ci wa ‘yan fansho tuwo aƙwarya.
“Dole ne gwamnati ta daidaita fansho don daidaita duk wani ƙarin albashi mafi ƙaranci,” in ji shi.
A Katsina, wata gamayyar ƙungiyoyin farar hula (CSO) ta yi Allah-wadai da tsarin fansho da ake amfani da shi.
Abdulrahman Abdullah, shugaban gamayyar, ya yi zargin cewa shirin yana amfanar masu kula da kuɗaɗen fansho fiye da waɗanda suka yi ritaya.
“Masu kula da fansho suna cin gajiyar sadaukarwar ma’aikata a duk lokacin da suka shafe suna aiki, wani lokacin yana ɗaukar sama da shekara guda kafin su samu kuɗaɗensu,” in ji Abdullah.
Ya ba da shawarar a horar da ma’aikata dabarun saka hannun jari kafin su yi ritaya, ta yadda za su yi amfani da kudaden tallafin da suke samu a matsayin jari don gudanar da ayyukan su.
Da yawa suna jiran watanni shida zuwa goma sha biyu don samun haƙƙoƙinsu, Abdullah ya kira tsarin “cin zarafin ma’aikata.”