‘Yan fashin daji sun yi awon gaba da ɗaliban Zamfara

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga sun sace ɗalibai huɗu na Kwalejin Nazarin Kimiyyar Lafiya ta Jihar Zamfara da ke garin Tsafe, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Tsafe.

Jaridar SpyeNews ta samu tabbacin aukuwar hakan daga majiyoyi daban-daban, cewa wasu ‘yan fashin daji sun afka garin Tsafe ran Talata da daddare inda suka kwashi ɗaliban kwalejin ciki har da ɗalibai mata da ke zama a wajen makaranta.

Majiyarmu ta ce ɗalibai biyar ne aka sace amma daga bisani ɗaya daga ciki ya kuɓuta sai ɓarayin suka tafi da mutum huɗu.

Idan za a iya tunawa, ko ‘yan kwanakin da suka gabata sai da ‘yan fashin dajin suka kai hari garin Tsafe inda suka kashe mutum uku ciki har da ɗan gidan tsohon kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Zamfara, Mamman Tsafe.

Harkokin garkuwa da mutane da neman kuɗin fansa na ci gaba da ta’azzara a yankin Aarewacin Nijeriya, inda kawo yanzu aka yi garkuwa da ɗaruruwan mutane.

Ya zuwa haɗa wannan labari, ƙoƙarin da aka yi don jin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sandan Zamfara, Muhammed Shehu kan wannan batu ya ci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *