
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙi amincewa da kasafin Naira biliyan 942 da Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) ta gabatar domin gudanar da ƙidayar gidaje da mutane a ƙasar.
Hakan ya biyo bayan tattauanawa da manyan jami’an NPC da Tinubu ya yi a ranar 24 ga watan Fabrairu a Fadar Shugaban ƙasa, inda ya nace akan sai dai a nami hanyar rage adadin kuɗin.
Wasu muryoyi sun bayyana cewa, Shugaba Tinubu ya nemi da sanya ƴan hidimar ƙasa (ƴan NYSC) a matsayin waɗanda zasu gudanar da aikin ƙidayar, wanda akwai yiwuwar hakan ya tabbata kuma ya taimaka wajen samun sauƙin kuɗaɗen da za a kashe.
Bayan zama da jami’an NPC ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Nasir Kwarra, Tinubu ya yi alƙawarin samar da kwamitin da zai daidaita kasafin ƙidayar da kuma halin tattalin arziƙin ƙasa.
A sanarwar da Kakakinsa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Shugaban ƙasar ya samar da kwamiti a yayin da ake shirin gudanar da sabon ƙidaya a Nijeriya, ya na mai ƙoƙarin ganin an cimma matsaya.
Ya ce, shugaba Tinubu ya koka ga yawan kuɗaɗen kasafin waɗanda adadinsu ya kusa kai tiriliyan ɗaya, ya na mai cewa lallai sai an samar da hanyoyin rage adadin.
Haka kuma lallai sai Hukumar Kula da Shaidar Ɗan ƙasa (NIMC) ta shiga cikin ɓangarorin da za su yi nazari game da aikin.