‘Yan jarida sun yi barazanar ƙaurace wa tattara sakamakon zaɓe a Kano

Daga WAKILINMU

‘Yan jarida a Jihar Kano sun zargi Hukumar Zaɓe, INEC, da zaɓen ‘yan tsiraru daga abokan aikinsu don sa ido kan sha’anin tattara sakamakon zaɓen gwamna da na majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar Asabar.

Da wannan ‘yan jaridar suka yi barazanar ƙaurace wa aikin tattara sakamakon zaɓen muddin ba a ɗauki matakin gyara nan take ba.

Sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na INEC, Adam Maulud, ya fitar ta nuna wasu ‘yan tsirarun ‘yan jarida aka yarda su lura yadda aikin tattara sakamakon zai gudana a ranar Lahadi.

INEC ta shirya soma tattara sakamakon zaɓen ne ya zuwa ƙarfe 2 na rana, na ranar Lahadi.

Da aka nemi jin ta bakinsa kan batun, Maulud ya ce hukumar ta ɗauki wannan mataki ne saboda dalilai na tsaro.

Jami’in ya ce rage adadin waɗanda za su saka ido kan lamarin tattara sakamakon ba a kan ‘yan jarida kaɗai ya taƙaita ba, har da ma masu sanya ido na ƙasa da ƙasa da sauransu.

A hannu guda, Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida reshen wakilai a jihar, Ibrahim Garba, ya buƙaci ‘yan jarida da su dakata, tare da umurtar ‘yan tsirarun da aka zaɓa kada su amsa gayyatar da aka yi musu.