‘Yan jarida suna da rawar da za su taka wajen magance ta’addanci a ƙasa – Farfesa Khalid Zaria

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An bayyana ‘yan jarida a matsayin wasu mutane da suke da muhimmanci a cikin al’umma, kuma waɗanda ke da rawar da za su iya takawa wajen magance tashe-tashen hankula da ta’addanci a Nijeriya.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shehin malamin nan masanin tarihi da harsunan Afrika, Farfesa Khalid Abdullahi Zaria, a wajen taron gabatar da littafin sa a ranar Lahadi a Agura Otal da ke Abuja, wanda ya rubuta akan rayuwar tsohon gwamnan Jihar Kwara, kuma tsohon shugaban majalisar dattawa ta takwas, Dr. Abubakar Bukola Saraki.

Farfesa Abdullahi ya yi nuni da cewa gwamnati za ta iya saka ‘yan jarida gaba don nemo hanyoyin magance matsalar tsaron da ake fama da shi a Nijeriya, musamman a yankin Arewa inda kashe-kashe da garkuwa da mutane suka yi ƙamari.

“Idan ana gwabza yaƙi tsakanin mutane biyu, shi ɗan jarida burin shi ya samo rahoto don nuna wa duniya wannan abu fa ba daidai ba ne, ko kuma kashe-kashen da ake yi ya yi yawa ya kamata hukumomi su ɗauki mataki,” inji Farfesa.

Farfesa ya kuma ƙara da cewa ɗan jarida mutum ne na kowa, kuma mai son bayyana gaskiya, inda ya ce shi ya sa wani lokacin saboda faɗar gaskiya ne har ake muzguna musu a ci mutuncin su.

“Har marin ɗan jarida ake yi idan aka ga zai faɗi gaskiya, idan kuma ya faɗa sai a ce saboda marin da aka yi masa ne ya faɗi abinda ya faɗa,” a cewar Farfesa Abdullahi Zaria.

Mawallafin littafin tarihin rayuwar Sanata Dr. Abubakar Bukola Saraki, kuma wanda ya wallafa littattafai 159 zuwa yanzu, ya gabatar da littafin wanda ya yi wa laƙabi da ‘Jarumi’ ne a ranar Alhamis 19 ga Disamba, 2021, daidai ranar da Sanata Bukola Saraki ke cika shekara 59 a duniya.