‘Yan Kano da Gombe sun lashe musabaƙar Ƙur’ani a Abuja

Daga BASHIR ISAH

An kammala musabaƙar Ƙur’ani na 2022 wanda gidan talabijin ɗin Gaskiya TV ya shirya da aka gudanar a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

Gasar wadda aka kammala ta a ranar Alhamis da ta gabata, ita ce irin ta ta farko da aka taɓa samu wata hukuma ko cibiya mai zaman kanta ta gudanar a ƙasa.

Alhaji Hamza Tanko wanda ɗan kasuwa ne kuma ɗan asalin ƙasar Ghana kuma ya shahara wajen hidimta wa al’umma da dukiyarsa, shi ne ya ɗauki nauyin gudanar da wannan musabaƙar karo na farko a Nijeriya. Inda ya bayyana cewa, soyayyarsa ga Alƙur’ani ya ƙarfafa masa shirya musabaƙa ta shekara-shekara a ƙasarsa Ghana wadda aka soma a shekarar da ta gabata.

Mubarak Aliyu, ɗan shekara 20 daga jihar Gombe shi ne ya zama gwarzon gasar wanda hakan ya sa ya samu kyautar kuɗi $5,000 da kuma kujerar Hajji inda zai je ya sauke farali yayin Hajjin 2022.

Mubarak ya gaza ɓoye farin cikinsa dangane da wannan nasarar da ya samu, tare da kira ga abokan karawarsa da su ci gaba da dagewa game da karatun Ƙur’ani har ma su wuce inda shi ya kai a matsayi.

A hannu guda, Aisha Abubakar Hassan, ‘yar shekara 16 daga jihar Kano, ita ce ta zo ta ɗaya a rukunin izifi 30 a ɓangaren mata. Ita ma ta samu kyautar kuɗi $5,000 da kujerar Hajji.

Waɗanda suka zo na biyu da na uku, sun samu kyuatar kuɗi $4,000 da $3,000 tare da kujerar Hajji ga kowannensu. Yayin da waɗanda suka zo na huɗu da na biyar suka tashi da kyautar kuɗi ta $2,000 da $1,000.

A cewar Kodineto na musabaƙar a shiyyar Afirka ta yamma, Abdulshakur Abbas, mutum biyar ɗin da suka yi nasara a gasar su ne za su wakilci Nijeriya yayin musabaƙar da aka shirya a tskanin ƙasashen Afrika ta yamma wadda za a gudanar watan gobe a ƙasar Ghana.

Taron rufe gasar ya samu mahalarta daga kusa da nesa, ciki har da wakilin Sarkin Musulmi da sauransu.