’Yan kasuwa a Nijeriya sun ƙalubalanci ECOWAS kan kan rufe iyakar Ghana

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Larabar da ta gabata ne wasu ‘yan kasuwa a Nijeriya suka nuna fushinsu a game da yadda Ƙungiyar Gamayyar Ƙasashen Afirka ta ECOWAS ta ja bakinta ta tsuke game da maganar rufe bodar ƙasar Ghana. Abinda a cewar ‘yan Kasuwar ya zama tamkar hawan ƙawara ne a kan dokar nan da ta ba wa duk ‘yan Afirka  ‘yancin zirga-zirga a ko’ina a Afirka. 

Shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar Nijeriya mazauna ƙasar Ghana (NUTAG), Mista Chukwuemeka Nnaji, shi ya bayyana haka a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da kamfanin dillancin labarai (NAN), ranar Larabar nan.

Hakazalika, Mr Chukwuemeka Nnaji, ya kuma nuna rashin jin daɗinsa a kan yadda mahukuntan ƙasar Ghana suka garƙame wa wasu ‘yan Nijeriya shagunansu a ƙasar Ghana tun watan Maris ɗin shekarar 2020 har yanzu ba su yi wani abu a kai ba. 

Kuma ya ƙara da cewa, har yanzu bodar ƙasar Ghana tana nan a garƙame. Abinda ya kawo wahala da jigata ga duk wani mazaunin ƙasar da yake fita yawon ci-rani ko fatauci. Domin a cewar sa, ‘yan Nijeriya da ‘yan sauran ƙasashen Afirka waɗanda suka yi gangancin bin hanyar bodar ƙasar Ghana, suna fuskantar wulaƙanci da tozarci da tsangwama a hannun jami’an tsaron ƙasar da jami’an shige da ficen ta, Immigirashan.

Idan ‘yan kasuwar za su shiga Ghana, banda ƙarin nisan tafiyar da zagayen da mutum zai yi don guje wa jami’an tsaro, sannan hanyoyin ma kansu suna da haɗari. Sai kuma batun kuɗaɗen da za ka biya jami’an tsaron. Aƙalla za a kashe Naira dubu 20 zuwa Naira dubu 100 don ba wa jami’an su ƙetarar da mutum boda. Sannan kayan da aka saro za a shiga ko fitar da su daga ƙasar sukan yi watanni kafin su isa, maimakon da kwana 5 suke yi kawai. A cewar sa hakan ya taimaka wajen ƙarin tsadar kayan masarufi. 

Daga ƙarshe ya yi kira ga mahukuntan ECOWAS da su kawo ɗauki don kawo sassauci a kan wannan mawuyacin hali da ‘yan kasuwar suka tsinci kansu na tsahon watanni 18 kenan.