‘Yan kasuwa sun buƙaci a ɗaga farashin fetur

Daga AISHA ASAS

‘Yan kasuwar man fetur sun ce bisa la’akari da yadda abubuwa ke tafiya a kasuwar ɗanyen mai ta duniya, kamata ya yi farashin fetur kan lita guda ya zama tsakanin N185 zuwa N200 a Nijeriya.

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna an samu tashin farashin fetur a kasuwar mai ta duniya a makon da ya gabata wanda hakan ya sanya ‘yan kasuwar nuna damuwarsu kan yadda ba a aiwatar da cikakken shirin sakar wa ‘yan kasuwar mara ba a harkar man fetur, lamarin da ya hana samun sauyin farashin litar fetur sama da watanni biyu

A hirar da jaridar Punch ta yi da shugabannin ‘yan kasuwar, jagororin sun ce hauhawar farashin mai da akan samu a kasuwar mai ta duniya ya dawo da tallafin mai.

A ranar 11 ga Janairun da ya gabata, Punch ta ruwaito cewa tashin farashin mai a duniya ya haifar da tsadar shigo da mai daga ƙetare wanda hakan ya yi kama da komawa zamanin tallafin mai da aka janye.

Tun bayan ƙarin farashin mai na ƙarshe da aka yi a Nuwamban 2020 a Nijeriya, farashin ɗanyen mai a kasuwar mai ta duniya ya ƙaru da kashi 43 cikin 100 inda ya cilla daga $41.51 kan kowane ganga guda zuwa $59.34 a Juma’ar da ta gabata.

Bayan haka, ‘yan kasuwar sun sa ran ganin an yi ƙarin kuɗin mai a Disamban da ya gabata don samun daidaito da ƙarin farashin da ake samu a kasuwar mai ta duniya amma hakan bai faru ba.

Maimakon haka, Gwamnatin Tarayya ta sanar da rage farashin fetur da N5 wanda ya soma aiki a ranar 14 ga Disamban da ya gabata lamarin da ya cika ‘yan kasuwar da mamaki. ‘Yan kasuwar dai na ganin abin da ya fi dacewa shi ne a ɗaga farashin man tsakanin N185 da N200 kan lita guda.

A halin da ake ciki, ana sayar da man kan lita guda N160 zuwa N165 ne galibin gidajen man da ke Legas.

Babban Sakataren Ƙungiyar Manyan ‘Yan Kasuwar Mai ta Nijeriya, Mr Clement Isong, ya ce mambobin ƙungiyarsu sun damu da cigban fannin mai da ma ƙasa baki ɗaya.