Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
’Yan kasuwar man fetur, a ranar Juma’a, sun bayyana cewa farashin man fetur wanda matatar man Dangote ke samarwa ya kai Naira 1,015 zuwa Naira 1,028 kan kowace lita, gwargwadon adadin da ake saya.
A kan haka ne dillalan suka sha alwashin shigo da mai tare da sayar da shi ƙasa da farashin matatar Dangote da kuma farashin da Kamfanin Man Fetur na Nijeriya ke sayarwa.
Alƙaluman da ƙungiyar ’yan kasuwa na ‘Major Energy Marketers Association of Nigeria’ ta fitar a ranar Alhamis sun nuna cewa farashin man fetur ya kai N978.01 kan kowace lita a ranar 31 ga Oktoba, 2024.
Ya bayyana cewa farashin man dizal ya kai Naira 1,069.97 a lita, yayin da na man jiragen sama ya kai N1,119.67 a lita.
Farashin waɗannan kayayyaki ya zarce farashin kayayyakin da ake shigowa da su daga gaɓar tekun Nijeriya.
Tun bayan da matatar man Dangote ta fara fitar da tataccen man fetur a cikin gida, ta ƙi bayyana haƙiƙanin farashin man duk da buƙatuwar hakan.
Sai dai wani babban ɗan kasuwar da ya zanta da ɗaya daga cikin wakilanmu da ya nemi a sakaya sunansa saboda rashin ba da izinin yin magana a kan lamarin, ya tabbatar da cewa farashin man fetur daga matatar Dangote ya zarce na man da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
A cewar jami’in, matatar man a halin yanzu tana sayar wa ‘yan kasuwar man da suke saya kaso a kan Naira 1,015 a lita sai kuma ƙananan masu saye kan Naira 1,028.
Babban ɗan kasuwar ya kuma bayyana cewa wasu jiragen fakon mai uku ɗauke da man fetur sun iso kwanan nan kuma an sallame su a tashoshin jiragen ruwa da ke kan iyakokin ƙasar.
“Dangote yana sayar wa masu saye da yawa akan N1,015 a lita, amma ga ‘yan kasuwa da ba sa saye da yawa, matatar man tana sayar da kan N1,028 a lita.
“Amma man da ake shigo da shi ya fi na Dangote arha, kuma shi ya sa yake yin duk mai yiwuwa don ganin gwamnati ta dakatar da shigo da man fetur,” inji dillalin.
Da suke tsokaci kan wannan lamari, ‘yan kasuwa a ƙarƙashin ƙungiyar masu sayar da man fetur ta Njjeriya sun sha alwashin cewa za su sayar da mai daga ƙasashen waje ƙasa da farashin da matatar ta Dangote ke bayarwa.
ƙungiyar ta ce, man fetur ɗin kuma za ta yi arha fiye da na NNPC.